<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>192</hymn_number>
<title>Ya Yesunmu, Mun Taru Wurinka LW192</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Yesunmu, mun taru wurinka.
 Ka ji roƙonmu, mu ne ƴaƴanka.
 Ya Ruhun Allah, buɗe zuciyarmu,
 Yi aikinka, ya Ruhu, cikinmu.

[V2]
 2) Bayyana kanka cikin ƙaunarka.
 Bishe mu kuwa ta wurin Ruhunka.
 Mai Taimako fa cikin zuciya,
 Zai buɗe mana dukan gaskiya.

[V3]
 3) Ruhunka Yesu, Ruhunka kaɗai
 Zai tsarkake zukatanmu sarai.
 Ikonsa ne zai juye nufinmu,
 I, daga ƙeta zuwa Allahnmu.

[V4]
 4) Ruhun bangaskiya, Ruhun ƙauna kuwa,
 Ruhu Mai Tsarki, kyautar hannunka,
 Shi zo, shi sauko bisa dukanmu,
 Ikonsa kuwa shi zauna cikinmu.</lyrics>
</song>